✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsin Rayuwa: An gudanar da sallar neman sauki

wannan lokaci shi ne yafi dacewa da al'umma su tattaru don karfafa imanunsu tare da rubanya ibada

Al’ummar Musulmi a garin Zariya sun gudanar da Sallah ta musamman don neman dauki daga Allah bisa halin matsi da ake ciki a kasar nan.

Sallar da aka gudanar da ita a masallacin idi na Filin Mallawa da ke Tudun wlWada Zariya ta samu halartar Musulmi maza da mata daga sassa daban-daban na birnin Zariya.

Wanda ya jagoranci sallar kuma Babban Limamin Masallacin Juma’a na Bakin Kasuwar Tudun Wada Zariya, Liman Muhammad Sani Labudda, ya ce dole ne Musulmi su mike don neman tallafi wajen Allah kan halin da jama’a ke ciki.

Limamin ya ce halin da ake ciki ya yi tsanani inda a kullum farashin kayayyakin masarufi sai kara hauhawa yake yi, don haka ya zama wajibi ga Musulmi da su koma ga Allah musamman ganin ana tunkarar azumin watan Ramadan.

Da yake jawabi bayan kammala sallar, Shugaban Kungiyar Makarantun Islamiyya na Zariya, Suleiman Ibrahim, ya ce wannan lokaci shi ne yafi dacewa da al’umma su tattaru don karfafa imanunsu tare da rubanya ibada don samun saukin rayuwa.

Malam Suleiman ya roki daukacin al’ummar Musulmi da su rika kokarin bayar da sadaka ga mabukata da kuma marasa shi a matsayin wata hanya ta neman gafarar Allah.

Tun farko, Sheikh Muhammad Dan Tine Habibi da Mallam Umar Dikko Mai Shinkafa na Kungiyar Fitiyanul Islam Reshen Zariya, sun jaddada muhimmancin gudanar da irin wannan ibada a duk lokacin da al’umma suka sami kan su a wani mawuyacin hali.

Sun roki Musulmi da su ci gaba da tsoron Allah a dukkan al’amuransu tare da kokarin tuba bisa zunubansu don kauce wa fushin Mahalicci.