✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta lakume bishiyoyin kwarar manja 4,000 

Gonar da ta kone takan zamar jarkoki 50 na manja a duk sati da kuma ton 500 na abarba a shekara

Wata gobara ta lalata eka 50 na bishiyoyi dubu hudu na kwarar manja da kuma eka biyar na noman abarba a wata gona a Jihar Osun.

Mai gonar, Mista Rufus Jegede, ya bayyana cewa a kowane mako karafariyar gonar mai suna Royal Farm tana samar da jarkoki 50 na manja a duk mako, wato kimanin jarkoki 2,600 a shekara.

Ana samar da ton 500 na abarba a kowace shekara a gonar ta Gonar Royal Farm da ke kauyen Akeredolu a kusa da garin Osu cikin Karamar Hukumar Atakumosa.

Amma a cikin hirarsa da ’yan jarida a ranar Lahadi, ya ce bana babu abin da za a girba a gonar a dalilin tashin wutar.

Ya bayyana cewa wutar ta tashi ne a ranar Juma’a inda ta lalata wadannan bishiyoyi da aka kiyasta kudinsu ya haura Naira miliyan 150.

Amma ya yi zargin cewa an cinna wutar ce da gangan, domin a cewarsa sau uku ke nan ana yin barazanar kona gonar a cikin shekaru tara da kafuwarta.

Mista Rufus Jegese ya nuna mamakin ganin gonar tasa kadai ce wutar ta lakume.

Ya kar da cewa jami’an tsaro sun kama wani mutumi da ake zargi da cinna wutar gonar.