✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau ake fara bukukuwan mika mulki ga sabuwar gwamnati

Tinubu zai karbi rantsuwar fara aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16 a ranar 29 ga Mayu, 2023.

A yau Alhamis, 25 ga Mayu 2023, ake fara bukukuwan mika mulki ga shugaban kasan Najeriya na 16, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wanda zai karbi mulki daga Shugaba Buhari a ranar Litinin a hukumance.

Shugaba Buhari zai ba wa Tinubu lambar girmamawa ta kasa ta GCFR, wadda ta kebanta ga shugabannin kasa, a yayin bikin da za a fara a Abuja ranar Alhamis.

A yayin bikin ne kuma ba wa Mataimakin Shugaban Kasa mai jiran gado, Sanata Kashim Shettima lambar GCON wadda ake ba wa mataimakan shugaban kasa.

A ranar ce kuma ake sa ran za mika kundin bayanan ayyukan gwamnati mai barin gado ga sabuwar gwamnatin da za a rantsar a ranar Litinin.

Sai ranar Juma’a da za a gudanar da addu’o’i na musamman a Masallacin Juma,’a na kasa da ke Abuja.

Ranar Asabar kuma a gudanar da jawabai, wanda cikin masu jawabin har da tsohon Shugabna Kasar Kenya Uhuru Kenyata.

Ranar Lahadi za a gudanar da iba ta musamman a Babban Cocin Kasa.

Litinin 29 ga watan Mayu kuma a rantsar da sabon shugaban kasa tare da mataimakinsa a dandalin Eagle Square da ke Abuja.

A daren ranar za a gudanar da liyafar alfarma inda za a karbi bakuncin shugabannin kasashe da suka halarci bikin.

Tuni dai Shugaba Buhari ya yi jawabin bankwana da godiya ga ministocinsa, a yayin zamansu na karshe Malisar Zartarwa ta Kasa a ranar Laraba, duk da cewa ya bukaici su ci gaba da aiki har zuwa karfe 12 na daren ranar Lahadi.

Buhari ya kuma jinjina wa hadimansa da sauran ma’aikatan fadar shugaban kasa, tare da yin kira da a ba da cikakken hadin kai ga Shugaban Kasa Mai Jiran Gado, Bola Tinubu.