✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jajibirin mika mulki: Buhari na neman biyan bashin N539bn na aikin shari’a

Kwana hudu kafin ya mika mulki, Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi sahalewar Majalisar Dattawa domin biyan bashin Naira biliyan 539 na aikin shari’a da ake…

Kwana hudu kafin ya mika mulki, Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi sahalewar Majalisar Dattawa domin biyan bashin Naira biliyan 539 na aikin shari’a da ake bin Gwamnatin Tarayya.

A takardar da ya aike wa Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan, Buhari ya bayyana cewa kudaden sun hada da Dala miliyan 566.8 da Fam miliyan 98.6 da kuma Naira biliyan 226.3.

Ya ce za a biya bashin ne ta hanyar raba takardun lamuni, kamar yadda, “Ranar 29 ga watan Maris, 2023, Majalisar Zartawar ta Kasa ta amince a biya manyan basukan aikin shari’a da ake bin Hukumomi da Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya ta hanyar takardun lamuni, daga bisani za a biya a hankali daga kasafin kudi

“Don haka ake neman sahalewar majalisa, kuma Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Kasa tare da Ministar Kudi za su bayar da duk bayanan da ake bukata.”

A ’yan makonnin nan dai shugaban da ministocinsa na daukar wasu muhimman matakai da suke bayyana cewa bai saba doka ba, duk da cewa wa’adin gwamnatin ya kawo karshe.

Amma wasu masana na ganin duk da cewa hakan ba laifi ba ne, amma maimakon daukar matakan ciwo bashi da bayar da mukamai ko kwangila a kurarren lokaci, kamata ya yi a bar wa sabuwar gwamnati  da za ta kama aiki daga ranar Litinin. 

Wani masanin Kiminiyyar Siyasa, Dokta Abdullahi Ibrahim, ya ce babu laifi gwamnati mai barin gado ta dauki mataki a kan wasu abubuwa, amma duk da haka, gara ta bar wa gwamnatin da za ta shigo ta yanke shawara a kansu. 

“Misali shi wannan maganar kudaden shari’ar ai sun yi watanni ko ma shekaru, don haka dole a zargi gwamnati mai barin gado da yin rufa-rufa kan dalilin neman biyan kudaden a yanzu.

“Wasu ma na iya tunanin cewa an riga an kashe kudaden kafin amincewar majalisar, cika ka’ida kawai ake son yi yanzu.

“Gwamnati abu ne mai dorewa, kuma dai Jam’iyar APC ce za ta ci gaba da mulki, to mene ne dalilin wannan saurin?” 

 

Sagir Kano Saleh, Abdullateef Salau & Muideen Olaniyi