Hedikwatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta yi jana’izar sojojinta akalla 60 da suka rasa rayukansu sanadiyyar harin ta’addanci.
An gudanar da jana’izar jami’an tsaron ne a garin Tiliya da ke jihar Tawa kusa da iyakar kasar da Mali,a ranar Talata, washegarin da suka gamu da ajalinsu ne a hanyarsu ta kai dauki ga wasu jami’an tsaron da ’yan ta’adda suka afka wa.
- ’Yan bindiga sun kashe kansila a Katsina
- DAGA LARABA: Me Ya Sa Waɗanda Suka Kammala Jami’a Ke Komawa Sana’ar Girke-Girke?
Alkaluman mamatan da hedikwatar tsron ta bayar sun nuna soja 29 suka kwanta dama, amma wadanda suka halarci jana’izar sun ce gawarwakin sun haura 60.
Wadanda aka yi wa jana’izar tasu dakarun rundunar ta musamman da ke fada da ayyukan ta’addanci ne daga yankin Tiliya mai makotaka zuwa yankin Menaka da ke cikin Mali.
Rahotanni sun nuna mayakan kungiyar EIGS mai ikirarin jihadi a yankin Sahel, sun hallaka sojojin ne ta hanyar dasa ababen fashewa da kuma amfani da motoci makare da ababen fashewa.