✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe kansila a Katsina

’Yan bindigar sun kashe Samaila Buhari Mairago a yayin da yake shirin gudanar da aikin sintiri a matsayinsa daya daga cikin jami'an samar da tsaro…

’Yan bindiga sun kashe wani kansila suka sace makwabcinsa a karamar hukumar Funtua ta Jihar Katsina.

Shaidu sun ce ’yan bindigar sun kashe Kansilan gundumar Nasarawa, Hon Samaila Buhari Mairago ne bayan dawowarsa daga ofishin ’yan sanda inda ya karbo bindiga domin gudanar da sintiri a matsayinsa na daya daga cikin jami’an samar da tsaro da gwamnatin jihar ta horas.

Wani makwabcinsa, Malam Musa Maibulo, ya ce bisa alama maharan sun shigo yankin ne da nufin sace wani, amma tsautsayi ya fada kan kansilian a daren na Litinin.

Malam Musa ya ce, “babu wanda ya lura, kowa na gudanar da harbokinsa ba tare sanin cewa bata-garin sun shigo ba.

“Kansilanmu Samaila Buhari wanda ke cikin masu sintiri ya je ofishin ’yan sanda na Makera ya dauko bindigarsa domin aikin sintiri yadda suka saba; amma aka yi rashin sa’a, ya je shiga gidansa, sai ’yan bindigar suka lura da bindigar da yake rataye da ita, shi ne suka bude masa wuta,” suka dauke bindigar suke tsare nan take.

Ya ce sai “bayan tserewarsu ne muka gane cewa sun sace wani makwabcinmu mai suna Malam Samaila Maikatako.”

Wani kawun mamacin, Abbas Isma’il wanda ya ce marigayin ya bar mace daya da ’ya’ya takwas, ya ce, “Abin takaici ne yadda ’yan bindiga suka addabi garin Funtua.

“Ko a ranar 3 ga watan Agusta sai da suka sace wata fitacciyar mai sayar da abinci, Hajiya Fati Mai Waina, kuma har yanzu ba su sako ta ba.”

Kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce rundunar ta samu rahoton abin da ya faru kuma tana gudanar da bincike a kai.