’Yan sanda da jami’an hukumar DSS sun kama ’yan canji guga 17 a kasuwar canjin kudade ta WAPA da ke Kano kan zargin ba su da rajista.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Usaini Gumel, ya sanar a ranar Laraba cewa wadanda aka kaman ba su da lasisin gudanar da hadahdar canjin kudade.
“Mun gudanar da aiki tare da hukumar tsaro ta DSS a kasuwar canjin kudade ta WAPA inda jami’anmu da suka kama mutane 29, amma daga bisani aka saki 12 daga cikinsu.
“Mun kama su da kudade da suka hada da Sefa 68,000 CFA da kuma Rupee 30 na kasar India.
- Majalisa Ta Yi Watsi Da Kudurin Hana Bankuna Cirar 0.5%
- Yau EFCC za ta gurfanar da Hadi Sirika kan zargin N2.7bn
“Duk wanda ake zargin sun amsa laifin kuma za a gurfanar da su a gaban kotu,” in ji kwamshinan an sandan.
A cewarsa, “Mun gudanar da samamen ne domin kawar da bata-garin da gudanar da harkar canjin kudi ba bisa ka’ida ba, wadanda ke sa harkar tangal-tangal a kasar nan.” (NAN)