Aminiya ta gano cewa akalla mutane 295 ne suka bakunci kiyama sanadiyyar hatsarin mota a watanni uku na farkon wannan shekarar.
Duk da cewa Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta ce wannan adadi ya zarce kididdigar da ta yi, sai dai ta gaza bayyana mana nata adadin a hukumance.
Binciken ya kirga iya haddura da manyan jaridun kasar nan suka bayar da rahoton afkuwar su a watanni ukun da suka gabata.
Mun gano cewa a tsawon lokacin mutane 315 sun samu munanan raunuka sakamakon hadarin mota a jihohi 24 da kuma Babban Birnin Tarayya.
Jihohin da aka samu rahoton haddura sun hada da:
- Osun
- Kwara
- Kaduna
- Sakkwato
- Neja
- Bayelsa
- Legas
- Kano
- Oyo
- Abuja
- Anambra
- Osun
- Kogi
- Binuwai
- Delta
- Ekiti
- Ebonyi
- Katsina
- Filato
- Ogun
- Ondo
- Edo
- Abia
- Taraba.
A yayin da ake samun haddura a wasu hanyoyin saboda rashin kyawunsu, wasu kuma ana samun hadduran ne saboda kyawunsu, wand6 ke bai wa direbobi damar yin gudun kere sa’a da watsi da dokokin tuki.
Abin da ke kawo yawan haddura
A cewar FRSC, gudu fice da kima da kuma daukar lodi fiye da misali ne kan gaba wurin haddasa hadurran kan tituna a Najeriya.
Sai dai kuma masana sun bayyaba rashin kyawun hanyoyi, gurbatar yanayi, rashin kula da ababen hawa, da tuki cikin gajiya a matsayin wasu daga cikin dalilan da ke janyo yawaitar hadurra a kan hanyoyin kasar.
Jonas Agwu, jami’in wayar da kan jama’a a FRSC ya ce: “Daga binciken da muka yi kan hadurra a Najeriya, manyan dalilai sin hada da lodin da ya fi ƙarfin mota, musamman yadda a ake makare tireloli da fasinjoji da dabbobi da kayayyaki.
“Sai kuma tuki a hannun da naka ba, gudun wuce sa’a da mummunar gajiya da kuma tafiye-tafiye a cikin dare.
“An kuma gano cewa direbobi na amfani da tayoyi marasa inganci, ga kuma rashin kula da motocinsu yadda ya kamata.”
Shi ma dai wani masanin harkokin sufuri, Farfesa Bamidele Badejo, a zantawarsa da Aminiya, ya dora alhakin karuwar hadurra a kan rashin kula da ababen hawa sakamakon tabarbarewar tattalin arziki a kasar nan.
Ya kuma ce akwai hatsarin da ke faruwa sakamakon rashin tsaro, inda a wani lokacin direba zai zabi ya kifar da motar maimakon ya mika kansa ga ’yan ta’adda masu satar mutane ko kuma ’yan fashi.
Farfesa Badejo, farfesa a fannin ilimin kasa da tsare-tsare, mai ra’ayi a kan harkokin sufuri kuma tsohon kwamishinan sufuri a jihar Legas, ya yi kira da a dubi yiwuwar sake fasalin hanyoyin da ake bi a fadin kasar nan.