Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwe, ta ceto fasinjoji 14 da wasu ’yan bindiga suka sace yayin da suke tafiya a kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo.
Sai dai uku daga cikin fasinjojin sun rasu, ciki har da direban motar.
- Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO
- Ɗalibai za su koma makaranta ranar Lahadi da Litinin – Gwamnatin Kano
A cewar sanarwar da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Catherine Anene, ta fitar a ranar Juma’a, lamarin ya faru ne a ranar 3 ga watan Afrilu, 2025.
Wasu ’yan bindiga sun farmaki motar a yankin Otukpo Burnt Bricks, inda suka buɗe wa direban da wani fasinja da ke gaba wuta, lamarin da ya tilasta direban tsayawa.
’Yan sanda tare da jami’an tsaro sun isa wajen da abin ya faru cikin gaggawa.
Sun iske direban da wani fasinja a cikin mota kwance cikin jini, amma an garzaya da su asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsu.
’Yan bindigar sun yi awon gaba da sauran fasinjojin zuwa cikin daji.
A ranar 4 ga watan Afrilu, ’yan sanda sun bi sahunsu zuwa cikin dajin inda suka yi musayar wuta, wanda hakan ya sa suke tsere suka bar mutanen da suka sace.
Biyu daga cikin waɗanda aka sace an yi musu rauni da adda kafin a ceto su.
An samu nasarar ceto mutum 14, amma ɗaya daga cikinsu ya rasu a asibiti, sauran kuma suna karɓar magani.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Steve Yabanet, ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, kuma ya sha alwashin kamo maharan.
Ya kuma buƙaci al’ummar Otukpo da su kai rahoton duk wanda suka gani da raunin harbin bindiga, domin an jikkata wasu daga cikin ’yan bindigar yayin artabu da jami’an tsaro.