’Yan sanda 11,000 ne za a girke domin tabbatar da tsao a zaben kananan hukumomi da za a gudanar a Jihar Kaduna a karshen mako.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Mudassiru Abdullahi, ne ya sanar da hakan a wurin taron sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin jam’iyyun siyasa da ’yan takara da masu ruwa da tsaki a zaben da za a gudanar da kananan hukumomi 23 na jihar.
“Yana da muhimmanci ku sani cewa a bangaren tsaro, mu ’yan sanda za mu tura akalla jami’ai 11,000 domin tabbatar da zaben ya gudana cikin lumana.
“Mun shirya wa zaben da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a kafin zaben, a lokacin zaben da kuma bayansa.
“Na umarci jami’an namu da su gudanar da ayyukansu cikin kwarewa da kare hakki kamar yadda doka ta tanada a yayin lura da zaben, sannan su sanya kafar wando da duk wani mutum ko kungiya da ta nemi kawo hargitsi a lokacin zaben.
“Dadin tsarin dimokuradiyya shi ne ya ba wa mutane damar su zaba wa kansu abin da suke so tun daga rumfar zabe.
“Idan har muka kasa ba su dama su zabi shugabanninsu ba tare da wani haufi ba, to da wuya mu iya samun nasara a sauran bangarorin tsarin na dimokuradiyya.”
A nata bangaren, Shugabr Hukumar Zabe ta Jihar Kaduna, Saratu Dikko Audu ta ce, “A shirye muke domin mu samar da sahihin zabe.”