’Yan Najeriya da aka kai yankin Port Sudan bayan barkewar yaki a Khartoum, babban birnin kasar Sudan suna hanyarsu ta dawowa gida Najeriya.
Da safiyar Juma’a aka fara kai su filin jirgi da ke birnin da ke yankin Tekun Bahar Maliya, inda za su hau jirgi zuwa gida, inda aka ba wa mata fifiko.
Wani dalibi daga cikin wadanda aka kai Port Sudan ya ce jirgin da zai dauko su ya riga ya sauka, har an kwashi wasu daga cikinsu filin jirgin.
Ya kara da cewa dalibai mata aka fara kwashewa a cikin motoci zuwa filin jirgin, saboda su aka ba wa fifiko a tafiyar.
Tuni dai sauran ’yan Najeriya da aka tsallaka da su zuwa kasar Masar bayan barkewar yakin Sudan suka fara isowa Najeriya.
Najeriya da sauran kasashe na ta rububin kwashe ’yan kasarsu daga Sudan, tun bayan barkewar yaki a ranar 14 ga watan Afrilu tsakanin sojoji da mayakan sa-kai na RSF a birnin Khartoum kan shugabancin kasar.
Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin na ta tsilla tsilla, a yayin da mutane ke ta tserewa suke daga Khartoum, bata-gari kuma na ta farfasa gidaje da cibiyoyin kasuwanci suna kwashe kayyai.