✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP ta sako ma’aikatan agaji 2 da ta sace

Sojojin Najeriya sun ceto biyu daga cikin ma’aikatan jinkai uku da mayakan kungiyar ISWAP suka yi garkuwa da su.

Sojojin Najeriya sun ceto biyu daga cikin ma’aikatan jinkai uku da mayakan kungiyar ISWAP suka yi garkuwa da su.

ISWAP ta yi garkuwa da ma’aikata uku na Kungiyar Lafiya ta Iyali (FHI360) da masu gadi biyu a masaukinsu da ke kauyen Fotoko da ke kusa da garin Gamborou Ngala a Jihar Borno.

Daya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa an sako biyu daga cikin ma’aikatan ne a ranar Laraba amma har yanzu daya daga cikin ma’aikatan yana hannun kungiyar.

Zuwa lokacin da muka samu wannan rahoto babu wata sanarwa a hukumance daga sojoji ko kungiyar tun bayan da aka samu labarin sace mutanen.

Amma kungiyar jinkan ta fitar da sanarwa cewa sojoji sun ceto biyu daga cikin jami’anta uku da ISWAP suka yi garkuwa su.