✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani yaro ya kashe mahaifiyarsa a Kano

Lamarin ya faru ne a yayin da aka sami jayayya tsakanin marigayiyar da dan nata

Wani karamin yaro a unguwar Rimin Kebe da ke Karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano ya daba wa mahaifiyarsa wuka lamarin da ya sa ta ce ga garinku nan.

Wani ganau mazaunin yankin, Muhammad Abdu, ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne yayin da aka sami jayayya tsakanin marigayiyar da dan nata da ake wa lakabi da Kwarangwal.

Ya bayyana cewa, “lokacin da muka ji ihunta mun garzaya gidan don kai dauki inda muka same ta kwace cikin jini male-male ga kuma yanka a jikinta.”

A cewarsa tuni wanda ake zargi ya cika wandonsa da iska bayan ya yi aika-aikar.

Haka kuma ya bayyana cewa daga baya an garzaya da marigayiyar Asibitin Koyarwa na Muhammadu Abdullahi Wase.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, inda ya ce zai yi karin haske akan lamarin daga bisani.