Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano a safiyar Juma’a.
Aminiya ta rawaito cewa akalla mutane 11 lamarin ya rutsa da su, kuma yanzu haka Jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Kano na ci gaba aikin ceto domijb da zakulo su.
- An harbe kwamandan sojoji har lahira a Kastina
- Ku fito ku yi bayani kan shirin Hakkin 2024 —Majalisa ga NAHCON
Mutane biyu daga ciki da aka samu nasarar kubutar da su dai na nan da ransu, kuma tuni aka garzaya da su asibiti domin ba su agajin gaggawa.