✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sun kashe mai jego bayan karbar kudin fansarta sau biyu

Masu garkuwa da mutane sun kashe wata mai jego, bayan da suka karbi kudin fansarta sau biyu daga hannun iyalansau.

Masu garkuwa da mutane sun kashe wata mai jego, bayan da suka karbi kudin fansarta sau biyu daga hannun iyalansau.

A ranar Alhamis aka tsinci gawar matar mai suna Kehinde Jibril, bayan wani manomi ya tsinci gawar tata da ta fara rubewa a cikin gonarsa da ke hanyar Ojoku a yankin Oja a Jihar Kwara.

’Yan bindigar sun yi mata kisan gilla ne bayan a makon jiya danginta da jama’ar unugwar sun fara shiga daji domin neman ta, amma hakar ba ta cimma ruwa ba.

Hakan ya kara jefa fama’a cikin damuwa game da halin da ta ke ciki a wajen masu garkuwa, wadanda sau biyu suna karbar kudin fansa da ya kai Naira miliyan 2.5 domin sako ta.

Jagoran al’ummar yankin, Baale Daudu Salaudeen Arolu, ya shaida wa wakilinmu cewa abin da ya faru ya girgiza daukacin al’ummar.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya ce “Mun samu labarin abin da ya faru, amma ba a kawo mana kara a hukumance ba”.

Masu garkuwa da mutane sun kutsa gidan mijin matar da ke unguwar Ago-Oja da ke Ilori inda suka tafi da ita suka bar jaririnta mai wata hudu da sauran ’ya’yanta.

A lokacin ne masu garkuwar suka sace wani dalibin Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Jihar Kwara, wanda daga bisani ya rasu a asibiti sakamakon runukan da suka yi masa, duk da cewa sun karbi Naira dubu 400 a kansa.