✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Ku kuka da kanku idan aka sake kashe dan Arewa a Kudu’

Mahara sun bindige ’yan Arewa takwas a kasuwar dabbobi ta Omumauzor da ke Jihar Abiya

’Yan Arewa sun yi kashedi da kakkausar murya cewa ’yan Kudu maso Gabas su kuka da kansu idan aka kara kashe ’yan Arewa a yankinsu.

Kungiyoyin ’yan Arewa sun yi gargadin cewa ba za su kara lamuntar cin kashin da ake wa ’yan uwansu a Kudu ba ne bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari kasuwar dabbobi ta Omumauzor da ke Jihar Abiya suka bindige ’yan Arewa takwas sannan suka kashe shanu 20.

Gargadin nasu na zuwa ne bayan a safiyar ranar Laraba tawagar gwamnatin jihar da Shugaban Ma’aikatan Gwamna, Farfesa Anthony Agbazuere, ya jagoranta sun ziyarci kasuwar domin yin ta’aziyya ga ’yan Arewa, da kuma gani da ido.

Gwamnatin jihar ta bakin Kwamishinan Yada Labarai, Eze Chikamnayo, ta yi “Allah wadai da harin da wadanda suka kai shi. Muna aiki tukuru don tallafa wa iyalan wadanda abin ya shafa, wadanda suka samu rauni kuma suna samun kulawa a asibiti.

“Mun fara aikin sauya wa ’yan kasuwar matsuguni da kuma biyan diyyar asarar da suka yi. Za kuma mu yi duk abin da ya kamata na ganin wadanda suka aikata wannan abu sun fuskanci hukunci,” inji shi.

Babu wanda aka kama

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Abiya, SP Geoffrey Ogbonna, ya tabbatar da harin, sai dai ya ce ba su da bayanan sunayen ’yan kasuwar dabbobin da maharan suka kashe.

A nasa bangaren, Babban Limamin garin Umuahia, Alhaji Mohamed Baraya, ya ce mutum tara ne aka kashe a harin, sai kuma shanu 20.

Cin kashin ya isa haka  —Kungiyoyin Arewa

Gamayyar Kungiyoyin ’Yan Najeriya (CNG) da Kungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (AYCF) sun yi tofin Allah tsine a kan kisan gillar, sannan suka ce Gwamnatin Jihar Abiya ta tabbata ta cika alkawuran da ta dauka na kamowa da hukunta maharan.

Kakakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman, ya ce dole ne gwamnatin ta gaggauta yin hakan, domin ’yan Arewa ba za su kara bari ana kai wa ’yan uwansu mazauna Kudu maso Gabas hari ana kashewa ba.

“Mun dade muna lura da irin kisan gillar da ake wa ’yan Arewa haka kawai a yakin Kudu maso Gabas, amma muke hakuri muna danne zuciyarmu.

“Amma wannan harin na Abiya ya kai mu bango, ba za mu yi shiru ba ana wa ’yan uwanmu cin kashi da kisan gilla a Kudu maso Gabas ba,” inji shi.

Shi ma a nasa banagaren, Shugaban AYCF, Yerima Shettima, ya yi tir da harin tare da bayyana damuwa kan yadda ake wa ’yan Arewa da ke gudanar da halastattun harkokinsu kisan gilla.

Yerima ya bukaci gwamnatin jihar da ta tababta ta cika alkawarinta na hukunta masu laifin, idan har tana so a samu zaman lafiya mai dorewa.

“AYCF na bibiya ta gani shin Gwamnatin Jihar Abiya za ta cika alkawuran da ta dauka na biyan diyya ga iyalan wadanda aka kashe, aka jikkata ko suka yi asara a harin.

“Muna fata wannan shi ne na karshe da za mu ji an kai wa ’yan Arewa hari, ba a Jihar Abiya ba kadai, a daukacin yankin Kudu maso Gabas, idan har ana so a samu zaman lafiya mai dorewa,” inji shi.

Shettima, ya jinjina wa jami’an tsaro da suka yi saurin kai dauki ga kasuwar da aka kai harin.

Daga Sagir Kano Saleh, Dalhatu Liman (Abuja), Maryam Ahmadu-Suka (Kaduna), Abdullateef Aliyu (Legas) & Linus Effiong (Umuahia)