Gasar Firimiyar Najeriya tana kara samun habaka ta bangarori da dama, tun daga tsarin filaye da biyan albashi da sauransu.
Babban abin da ke ci wa masu bibiyan harkokin Gasar Firimiyar tuwo a kwarya shi ne yadda kowace kungiya ala dole take yin nasara a gidanta, wanda yanzu wannan ma yanzu an samu sauyi.
- Minista: Cire sunana ya kara mini kaimi —Maryam Shetty
- An ceto daliban jami’a da aka yi garkuwa da su a Katsina
Yanzu ana zuwa har gida a lallasa kungiya, duk da cewa akwai sauran gyara da ake bukata a bangaren alkalan wasa.
Wani bangaren da ba a cika lura da shi ba shi ne yadda ake samun tururuwar ’yan kasashen waje musamman kasashen Afirka da ke zuwa taka leda a gasar ta Najeriya, wanda hakan bai rasa nasaba da inganta albashin ’yan wasan.
A yanzu haka ana shirye-shiryen fara sabuwar kakar gasar ta Firimiya, inda a nan Arewa Kungiyar Kano Pillars da Katsina United duk sun dawo gasar.
Binciken Aminiya ya gano cewa a kakar bara akwai sama da ’yan kwallo 20 ’yan wasu kasashen da suka fafata a Najeriya.
Aminiya ta ruwaito lokacin da dan kasar Brazil, Alberico Barbosa Da Silva ya taka leda a Gasar Firimiyar a Kungiyar Ifeanyi Ubah, inda ya kwashe shekara biyu.
Har yanzu kuma kocin Kungiyar Bandrezzer da ke Jihar Legas mai suna Rafael Everton dan kasar Brazil ne, kuma ya dade yana horar da ’yan wasa a kungiyoyi daban-daban a Najeriya.
Daga cikin ’yan wasan da muka kalato akwai: Bassa-Djeri Sabirou
Sabirou dan kasar Togo ne da yanzu yake taka leda a Kungiyar Enyimba, wadda ta lashe Firimiyar kakar bara.
Haifaffen garin Sokode ne, inda ya fara kwallo a Kungiyar Tchaoudjo kafin ya dawo Enyimba a shekarar 2020.
Ya fara wakiltar kasarsa ta Togo a shekarar 2017.
Jean Efala
Efala fitaccen suna ne a Gasar Firimiyar Najeriya, inda ya dade yana tsaron gida, yana hana ’yan wasan sakat.
Yanzu shi ne mai tsaron gidan Kungiyar Akwa United FC.
Dan kasar Kamaru, kuma yana cikin ’yan wasan kasar Kamaru bayan ya kasance gola mai hazaka a tawagar kasar na ’yan kasa da shekara 20.
Sauran sun hada da Mohammed Aminu dan kasar Ghana mai buga kwallo a Kungiyar Gombe United da Mohammed Hamza shi ma dan Ghana ne da ke Kungiyar Niger Tornadoes da Farouk Mohammed na Kungiyar Ribers United wanda shi ma dan Ghana ne.
Sai Golan Ribers United FC mai suna Albert Korbah dan kasar Laberiya, sai Denis Ndasi na Kungiyar Ribers United wanda dan Kamaru ne.
Akwai Mohammed Shiraz na Kungiyar Rivers United da Emmanuel Ampiah na Ribers United da Mutawakilu Seidu na Kungiyar Rangers International wadanda dukkansu ’yan Ghana ne.
Charles Tambe da ke Kungiyar Shooting Stars dan kasar Kamaru ne, sai Karim Abdoulaye wanda yanzu yake kungiyar Dakkata FC, wanda dan Jamhuriyar Nijar ne.
Sai Paul Ackuah na Kungiyar Rivers United da Nana Bonsu na Rangers International da Abdul Bashiru na Kungiyar Sunshine Stars FC da Eric Asamoah-Frimpong na Kungiyar Niger Tornadoes da Desmond Agbekpornu na Kungiyar Shooting Stars dukkansu ’yan Ghana ne.
A Kungiyar Kwara United akwai dan wasa Yakubu Ahmed dan Jamhuriyar Nijar ne da Jammeh Daddy wanda yake Kungiyar El-Kanemi Warriors wanda dan kasar Gambiya ne da Mark Gibson wanda yake Ribers United wanda shi ma dan Laberiya da sauransu.
Sai dai Aminiya ta lura cewa ’yan wasan kasar Ghana sun fi yawa a cikin ’yan wasan na kasashen waje.
A wani labarin daban, ana samun ’yan wasan Najeriya da suka buga kwallo a kasashen waje suna dawowa gida Najeriya domin ci gaba da taka leda.
Tsohon Golan Kungiyar Enyimba ya kama gola a kungiyoyi da dama a kasar waje, kafin ya bar Kungiyar Hapoel Afula a shekarar 2020 ya dawo Kwara United.