Akwa United ta zama zakara a Gasar Firimiyar Najeriya ta bana bayan samun nasara da ta yi a kan MFM FC da ta je mata bakunta Uyo.
Wannan ne karo na farko da kungiyar, wacce ake yiwa lakabi da Promise Keepers, ta lashe gasar tun bayan kafuwarta shekaru 25 da suka gabata.
Bayan wasan mako na 37 wanda aka tashi 5-2, Akwa United ta hada maki 71, inda ta bai wa Nasarawa United (wacce za ta yi nata wasan da Enugu Rangers ranar Litinin) da ke mataki na biyu tazarar maki 9.
Dan wasa Charles Atshimene ya yi bajinta inda ya zura kwallaye uku yayin wasan, wanda aka fafata ranar Lahadi a filin wasa na Godswill Akpabio.
A bana ne Akwa United ta jera wasanni 18 ba tare da an doke ta ba, kuma a gasar ce ta kafa tarihin jera wasanni mafi yawa ba a jefa mata kwallo ba a raga.
Haka kuma, wannan shi ne karo na biyu a tarihi da kocin kungiyar, Kennedy Boboye, ya lashe gasar – a baya ya horar da kungiyar Plateau United wacce ita ma ta lashe gasar a karon farko a tarihi a shekarar 2017.
Kungiyar tana fatar tsawaita jera wasanni tara da ta buga ba tare da an doke ta ba a wasanta na karshe na gasar bana da za ta kai wa Lobi Stars ziyara a ranar Alhamis.