Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta dauki sabbin ’yan wasa 22 daga kungiyoyi daban-daban don tunkarar sabuwar kakar wasanni ta bana.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran kungiyar, Idris Malikawa, ya fitar a ranar Laraba.
- ’Yan bindiga sun harbe sojar ruwa, sun sace danta a Jos
- Abin kunya ne ga Buhari ya mika mulki ga ’yan adawa a 2023 – Shugaban APC
“Mun kammala atisayen daukar sabbin ’yan wasa wanda mai horaswa Evans Ogenyi ya jagoranta kuma tuni muka dauki ’yan wasa biyar daga ajin matasa na Kano Pillars.
“Mun kuma dauki ’yan wasa 17 daga kungiyoyi daban-daban don hada su da ’yan wasa 18 da muka bari a kungiyar a kakar wasan da aka kammala.
“Da wannan nake tabbatar da cewa za mu samar da kungiyar gagara-badau a kaka mai zuwa,” in ji shi.
Malikawa, ya ce za a fara yi wa ’yan wasan gwajin lafiya kafin a yi musu rajistar kasancewa ’yan wasan kungiyar.
Sai dai ya yi gargadin cewa duk dan wasan da aka samu ba shi da cikakkiyar lafiya ba za a dauke shi ba.
Kano Pillars dai na daga cikin kungiyoyin kwallon kafa hudu da suka fada ajin gajiyayyu, bayan gaza samun makin da ake bukata a Gasar Firimiyar Najeriya.
Hukumar gudanarwar kungiyar ta nada Mista Evans Ogenyi a matsayin sabon mai horar da Pillars don yi mata garanbawul.