Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta ci gaba da jan ragamar Gasar Firimiyar Ingila, bayan doke Manchester City da ci biyu da nema.
Ƙungiyoyin biyu sun ɓarje gumi da yammacin ranar Lahadi, a filin wasa na Anfield.
- Mutum 4 sun rasu a hatsarin mota a hanyar Kaduna-Abuja
- Na gode wa Gowon kan yadda ya ceto rayuwata a hannun Abacha — Obasanjo
Cody Gakpo ne ya fada jefa wa Liverpool ƙwallo a minti na 12 da fara, yayin Salah ya ƙarƙare da ƙwallo ta biyu a minti na 78 a bugun fenariti.
Nasarar da Manchester City ta yi, ya adadin rashin nasarar da ta yi a wasanni bakwai a jere.
Wannan shi ne karon farko da Manchester City ta tsinci kanta a irin wannan mawuyacin hali, tun bayan da Guardiola ya karɓi ragamar horas da ƙungiyar.
Yanzu haka Liverpool na mataki na ɗaya s teburin gasar da maki 34 daga wasanni 13.
Ita kuwa Manchester City na mataki na na biyar da maki 23 daga wasanni 13.
Manchester ta yi rashin nasara a wasanni a Gasar Firimiyar Ingila ta bana.