A ranar Laraba ce aka kece-raini a tsakanin Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars da ta Katsina United a wasan raba-gardama na neman tsallakewa zuwa gasar Firimiyar Najeriya na kungiyoyi 8 da ke kira Super 8, inda a ciki za a dauki kungiyoyi hudu, biyu a Arewa, biyu a Kudu su dawo gasar Firimiyar.
A wasan karshe, Katsina United ta doke Kano Pillars da ci daya mai ban-haushi, inda Victor Mbaoma ya zura kwallo a ragar Kano Pillars a bugun finareti.
- Duniya na ci gaba da la’antar Isra’ila kan mamayar Falasdinawa a Jenin
- An sace masu aikin titin Kaduna-Kano su 4 a Tashar Yari
Sai dai duk da an doke Pillars, kasancewar Kungiyar DMD ta doke Kungiyar EFCC ta Abuja, sai kungiyoyin Katsina United da Kano Pillars suka samu nasarar tsallakawa zuwa Firimiya.
DMD ta lallasa EFCC da ci 3-0, inda Kano Pillars ta kara da maki shida, Katsina United ta samu maki shida, DMD da EFCC suka samu maki uku-uku.
A kakar bara ce Kungiyar Kano Pillars ta yi rashin nasara, inda ta koma rukuni na biyu na gasar Najeriya.
A tarihin kungiyar, wadda aka kafa a 1990, sau uku tana buga gasar rukuni na biyu a 1994 da 1999 da kuma bana.
Daga cikin dalilan da suka jawo faduwar Pillars, akwai samunta da laifi da hukumar shirya gasar ta yi bayan ta dawo taka leda a Filin Wasa na Sani Abacha, inda aka mayar da Pillars din Kaduna da buga wasan gida.
A wasan da aka buga na Arewa mafi zafi wato Northern Derby da Katsina United ce aka samu rikici, inda magoya bayan Pillars suka farfasa motar Katsina United.
Haka kuma a wasan da aka buga tsakanin Kano Pillars da Dakkada FC, Shugaban Kungiyar Kano Pillars na lokacin, Surajo Shu’aibu Yahaya wanda aka fi sani da Jambul ya yi wani laifin, inda aka kara zare wa Pillars maki uku, ya kama maki shida ke nan.
Ba don cire maki shidan ba, da kungiyar ba ta koma baya ba.
A lokacin Pillars ta daukaka kara don a dawo mata da makinta, amma ba ta samu nasara ba.
A daya bangaren, Kungiyar Sporting Lagos ce ta bayar da mamaki, inda ta samu nasarar zuwa gasar Firimiya a shekara biyu kacal da kafuwarta.
Kungiyar ta doke Stormers da ci 2-0, inda nan take ta samu tsallakawa zuwa Firimiyar.
An kafa kungiyar ce a shekarar 2022 a Legas, sai dai tana karfin dukiya, inda a watan Maris na bana ta shiga kwantiragi da kulob din Aarhus Fremad da ke kasar Denmark, sannan ta shiga yarjejeniyar buga rigunan wasa da Kamfanin Klasha.
Shugaban Kungiyar, Godwin Enakhena ne ya jagoranci Kungiyar MFM lokacin da ya dago ta zuwa gasar Firimiya, kamar yadda ya yi da Sporting Lagos a yanzu.
A lokacin hada wannan rahoto, ba a kammala daya wasann Kudu ba, inda za a samu kungiyar da za ta hadu da Sporting Lagos wajen tsallakowa gasar Firimiyar da kungiyar Heartland.