Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta kwashi kashinta a hannu yayin wasan mako na 20 da suka fafata da Gombe United a gasar Firimiyar Najeriya.
Gombe United ta yi wa Pillars da ake yi wa lakabi da sai masu gida ci daya mai ban haushi.
- ‘Ba abin da ake shukawa a Jihar Katsina sai lalata dukiyar gwamnati’
- Wani mutum ya karbi rigakafin Coronavirus sau 87 a Jamus
Filin wasa na Pantami shi ne dai ya karbi bakuncin wasan da ya gudana a ranar Lahadi 03 ga Afrilun 2022.
Dan wasa Barnabas Daniel ne ya zura kwallon a minti na 65 a karawar da aka shafe minti 90 ana bugawa tsakanin kungiyoyin da suka fito daga Arewacin Najeriya.
Nasarar da Gombe United ta yi ya sa ta koma mataki na 9 a teburin gasar da maki 27 a wasanni 20 da suka fafata.
Ita kuma Kano Pillars ta kasance a mataki na 13 da maki 24 a wasanni 20 da ta buga a kakar wasannin ta bana.
Yanzu haka dai Rivers United ita ce a matakin farko a teburin gasar da maki 43 a wasa 20 da ta buga.