✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Minista: Cire sunana ya kara mini kaimi —Maryam Shetty

Maryam Shetty ta ce ta rungumi kaddara, kuma cire sunanta ba zai sa ta butulci ba.

Matashiya ’yar Jihar Kano, Maryam Shetty wadda Shugaba Tinubu ya sauya bayan ya ayyana ta a cikin jerin ministocinsa ta ce ta dauki abin da ya faru a matsayin kaddara. 

Maryam Shetty, wadda maye gurbinta da Mariya Mairiga ta janyo surutai, ta ce ta dauki kaddara, kuma abin da ya faru ya kara mata kaimi wajen hidimta wa kasarta da kuma cimma burin da ta sa a gaba.

Shetty, wadda aka sanar da cire sunanta bayan ita da ’yan rakiyarta sun isa harabar Majalisar Dattawa domin a tantance ta, ta duk da hakan tana godiya ga Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da suka dacewarta da matsayin.

A cewarta, zabin nata alama ce ta gamsuwarsu da nagartarta da cancantarta a matsinta na matashiya ’yar Arewacin Najeriya, da za ta iya ba da gudunmuwa wajen kawo ci gaban kasar.

Bayan surutan da aka yi ta yi game da maye gurbinta ne ta fitar da sanarwa cewa, mika sunanta da aka yi da farko ya sa ta farin ciki marar misaltuwa,  amma “a matsayina na Musulma, na yi imani da kaddarar da ta biyo baya. Allah Ke bayar da mulki yadda Ya so, Ya karbe yadda Ya so.

“Har kwanan gobe ba zan gushe ba ina godiya ga Shugaba Tinubu da ya zabe ni da farko domin a wannan aiki. Sauya ni bai sa na karaya a aniyata ta hidimta wa kasata a duk matsayin da zan iya ba.

“Ba zan gushe ba ina godiya ga daukacin wadanda suka taya ni murna ko suka mara mini baya daga ko’ina; Ina kira da mu ci gaba da ba wa shugaban kasa goyon baya domin kasarmu ta samu daukaka.

“Duk da cwea an musanya sunana amma Allah kadai Ya san abin da zai faru nan gaba; Wadannan abubuwan da suka faru sun kara min kaimi da kuma imani cewa hidimta wa al’umma abu ne da bai kebanci masu mukami ba.

“Na kuma kara fahimta da imani cewa sauyi wani bangare ne na samun daukakar Najeriya.

“Ina rokon Allah Ya wa Shugaba Tinubu lafiya tare da matimakinsa, Sanata Kashim Shettima.

“Allah Ya kara wa Najeriya albarka! #webelieve!🇳🇬”