Ministar Fasaha da Al’adu, Hannatu Musawa, ta yi jimami tare da alhinin rasuwar fitacciyar jarumar Kannywood, Saratu Gidado, wadda aka fi sani da “Daso”.
Aminiya, ta ruwaito cewar Saratu Gidado ta rasu a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu a gidanta da ke Kano.
Ministar, cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun mai taimaka mata kan harkokin yada labarai, Nneka Anibeze, ta ce marigayiyar ta taka rawar gani wajen ci gaban al’adu a kasar nan.
Ta yaba da irin gudunmawar da marigayiyar ta bayar a masana’antar Kannywood.
Ta ce jarumar ta taka rawar gani wajen bunƙasa harshen Hausa da kuma al’adun Hausawa a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.
“Cikin kaɗuwa ina miƙa sakon ta’aziyyata ga iyalai da ’yan uwan Saratu Gidado, bisa rashinta da suka yi.
“Za a yi kewarta sosai. Ina addu’ar Allah Ya yafe mata kurakurenta. Allah Ya sa ta huta,” in ji ta.
Aminiya ta ruwaito cewa an haifi Saratu Gidado a watan Janairun 1968. Kuma ta rasu tana da shekara 56 a duniya.
Daso ta yi fice wajen fitowa a matsayin mai barkwanci a fina-finan Hausa na Kannywood.
Ta fara fitowa a cikin fim ɗin Linzami Da Wuta a shekarar 2000, wanda kamfanin Sarauniya Movies ya shirya.
Rawar da ta taka a fim ɗin ya sanya tauraronta ya haske, inda kowa ya santa.
Aƙalla ta fito a fina-finai sama da 1,000 a Kannywood.