✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Edgar Lungu: Za a yi zaman makokin kwana 7 a Zambiya 

Gwamnatin ƙasar ta ware ranakun ne domin nuna alhini da girmama Lungu.

Ƙasar Zambiya ta ayyana zaman makoki na kwanaki bakwai don girmama tsohon shugaban ƙasar, Edgar Lungu, wanda ya rasu a ranar Alhamis, 5 ga watan Yuni, 2025, a ƙasar Afirka ta Kudu.

Ya rasu yana da shekaru 68.

Lungu ya shugabanci Zambiya daga watan Janairun shekarar 2015 har zuwa watan Agustan 2021, lokacin da ya sha kaye a hannun shugaban ƙasa mai ci yanzu, Hakainde Hichilema.

Gwamnati ta sanar da cewa daga ranar 8 zuwa 14 ga wata Yuni, duk tutocin ƙasar za su kasance a ƙasa, sannan kuma an dakatar da duk wasu tarukan nishaɗi a wannan lokacin domin nuna alhini da mutunta tsohon shugaban.

Sakataren majalisar ministoci, Patrick Kangwa, ya bayyana cewa Shugaba Hichilema ya amince da yi wa Lungu jana’izar ƙasa.

An shirya dawowar gawarsa zuwa Zambiya a ranar Laraba mai zuwa.

Gwamnatin ƙasar ta ce Belvedere Lodge da ke babban birnin Lusaka ita ce cibiyar da aka ware don gudanar da makokin.

Kafin rasuwarsa, Lungu na ƙarƙashin kulawar likita a wani asibiti da ke Pretoria, Afirka ta Kudu.

Jam’iyyarsa ta Patriotic Front (PF) ta ce ya sha fama da wata cuta mai suna “achalasia” wata matsala ce da ke hana abinci wucewa a maƙogwaro yadda ya kamata.