✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon minista Ogbonnaya ya rasu

Tsohon ministan ya rasu bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha a gwamnatin Muhammadu Buhari, Ogbonnaya Onu, ya rasu.

Onu, wanda tsohon gwamnan Jihar Abiya ne, ya rasu bayan ya sha fama da gajeriyar rashin lafiya a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.

Idan za a tuna, tsohon ministan mai shekara 72 a duniya, ya fito takarar zaɓen fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaɓen 2023, amma ya sha kaye a hannun shugaba Tinubu.

Kafin rasuwarsa, Onu ya kasance ɗan siyasa, marubuci, sannan Injiniya.

Shi ne gwamnan farar hula na farko a Jihar Abiya, kafin daga bisani ya zama minista daga watan Nuwamban 2015 har zuwa lokacin da ya yi murabus a 2022.