✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPP

Shugaban jam'iyyar ya ce Kwankwaso ya ja musu rigingimu ba gaira ba dalili.

Jam’iyyar NNPP, ta bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya yi mata takarar shugaban ƙasa a 2023, ba zai tsaya takara a 2027 ba.

Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dokta Agbo Major, ne ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya mayar da martani kan wata magana da Buba Galadima ya yi.

Galadima, ya ce har yanzu Kwankwaso yana cikin NNPP kuma zai tsaya takara a 2027.

Galadima ya shaida wa manema labarai cewa: “Babu wani tabbaci da ke nuna cewa Kwankwaso yana shirin komawa APC. Za mu ci gaba da zama a NNPP har lokacin zaɓen 2027 ya zo. Muna kira ga ’yan Najeriya su mara masa baya.”

Amma shugaban NNPP ya musanta hakan, inda ya ce: “Kwankwaso da Galadima tun tuni aka kore su daga jam’iyyar. Ba su da hurumin magana a madadin NNPP ko amfani da ita domin yin takara,” in ji Major.

Ya bayyana cewa tafiyar NNPP da Kwankwasiyya ta ƙare tun bayan zaben shugaban ƙasa na 2023.

“Yarjejeniyarmu da Kwankwasiyya ta ƙare bayan zaɓen 2023. Ba za mu amince Kwankwaso ya dawo ba saboda matsalolin da ya janyo mana ba,” in ji shi.

Dokta Major, ya kuma zargi Kwankwaso da yunƙurin karɓe ragamar jam’iyyar ta ƙarfi da yaji.

“Kwankwaso ya canja tambarin jam’iyya zuwa na Kwankwasiyya ba tare da izini ba, kuma ya jefa mu cikin rikicin shari’u marasa tushe. Sai da aka kai kotu kafin INEC ta dawo da tambarinmu na asali,” in ji shi.

Ya ce Kwankwaso yana fatan sake samun damar tsayawa takara kamar yadda ya yi a 2023, amma hakan ba yiwuwa ba.

“Yana tsammanin zai sake samun tikitin takara kamar yadda ya samu a baya, amma hakan ba zai faru ba,” a cewarsa.

Ya ƙara da cewa: “An kori Kwankwaso da tawagarsa daga jam’iyya, kuma ba za mu karɓe su ba. Sun ci amanar jam’iyya. Ba shi da ƙarfin da zai iya ƙalubalantar Tinubu,“ in ji Major.

Sai dai ya amince cewa Kwankwaso yana da ‘yancin tsayawa takara, amma ya ce bai kamata ya jawo jam’iyyar NNPP rikici ba.

“Muna da masu sha’awar tsayawa takara a 2027, kuma za mu bi doka da tsarin jam’iyya wajen fitar da ɗan takara,” in ji shi.

Ya kuma buƙaci ’yan Najeriya da kada su saurari maganganun ’yan Kwankwasiyya.

“Kwankwaso ya kafa tasa jam’iyyar idan yana da muradin yin takara. NNPP ta wuce wannan matakin, ba za mu mayar da hankali kan rigingimun banza ba,” a cewar Dokta Major.