✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun yi wa mata fyade a Sabon Birni

Sun kai wa kauyuka da dama hari inda suka ci karensu babu babbaka

’Yan bindiga sun yi wa mata da dama fyade a kauyen Rambadawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.

Maharan sun auka wa kauyen Rambadawa ne a daren Litinin, inda suka rika lakada wa  mazauna dukan kawo wuka tare da yi wa mata fyade.

Da yake tabbatar da harin, wani dan banga a kauyen Adamawa da ke karamar hukuamr, Musa Muhammad, ya ce ’yan bindigar sun harbe mutum biyu har lahira a kauyen.

Maharan sun kuma auka wa kauyen Dantassako inda suka yi wa mazauna fashin dukiyoinsu.

Daga nan suka wuce zuwa kauyukan Nasarawa da Gidan Idi, suka kwace babura biyu.

Aminiya ta gano cewa gungun ’yan bindiga daban-daban ne ke sheka ayarsu a yankin Sabon Birni, kowanne da jagoransu.

Daga cikin jagororin ’yan bindigar da suka addabi yankin akwai Bello Turji, Nagona, Jambo Baki, Useini Dankwano da kuma Dan Bakkolo.

Hare-haren ’yan bindiga sun yi kamari a baya-bayan nan a yankin Sabon Birni inda suka taba kashe mutum 80 a dare guda suka kuma tarwatsa mutane da dama daga gidajensu.