✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sumar da basaraken Abuja da duka kan rashin cikar kudin fansa

’Yan bindiga sun sumar da wani basarake da suka sace a Abuja da duka saboda rashin cikar kudin fansarsa da suka nema

’Yan bindiga sun sumar da wani basarake da suka sace a Abuja da duka, saboda rashin cikar kudin fansarsa da suka nema

Zuwa yanzu Peter David, wanda shi ne Sarkin Fili a unguwar GRA da ke Mpappe, tare da ’ya’yansa uku sun shafe mako guda a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da su.

Aminiya ta ruwaito cewa a daren Larabar makon makon jiya ’yan bindigan kusan 30 suka shiga yankin Mpape suka suka sace Sarkin Filin, tare da matarsa da ’ya’yansa uku da karin wasu ’yan unguwar hudu.

Bayan kwanaki biyu sun sako matarsa Aisha, don ta nemo kudin fansa Naira miliyan 8 ne kawai daga miliyan 70.

A zantawarta ta waya da wakilinmu a matar ta ce iya hada Naira miliyan takwas ta iya samu daga milian 70 da ’yan bindigan suka nema kafin su sake mijinta da ’ya’yansu masu.

Aisha Peter ta ce “Na buga masu waya a safiyar yau Talata don sanar da su abin da muka iya hadawa tare da neman yin magana da mijina.

“Sai dai ’yarmu mai shekara 14 da na samu yin magana da ita ta sanar da ni cikin kuka cewa mijina baya iya magana a yanzu a sakamakon dukan da suka yi masa kan rashin cika masu kudin da su ke nema,” inji ta.

Ta ce sun ba ta karin mako guda na ta samar da kudin ko su kashe iyalan nata da ke hannunsu.

Aminiya ta samu labarin cewa babu mutum guda daga cikin hudu da a ke cigaba da garkuwa da su da ya samu dawowa gida.

Barayin na neman Naira miliyan hamsin daga wajen kowanne a cikinsu.