✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace masu zuwa nadin sarauta a Neja

Maharan na neman miliyan 17 a matsayin kudin fansa kafin sakin fasinjojin.

’Yan bindiga sun harbe wani direban bas suka sace mutane takwas da ke hanyarsu ta zuwa nadin sarautar Babban Limamin Bakarabonde a Masarautar Borgu a Jihar Neja.

Maharan suna kai farmakin ne a tsakanin yankunan Luma da Babanna da ke Karamar Hukumar Borgu a ranar Asabar.

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar na neman Naira miliyan 17 a matsayin kudin fansar wadanda suka sace.

Wadanda lamarin ya rutsa da su ne kan hanyarsu ta zuwa nadin sarautar babban limamin Bakarabonde a masarautar Borgu.

Shugaban Karamar Hukumar Borgu, Alhaji Sulaiman Yerima, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana lamarin a matsayin abun takaici.

Ya kuma tabbatar da cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci Naira miliyan 17 a matsayin kudin fansa kafin sako fasinjojin.