Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da akalla mutum bakwai a kauyen Igu da ke yankin Sherefe a Karamar Hukumar Bwari ta babban birnin tarayya.
An ruwaito cewa lamarin ya faru ne da daren ranar Alhamis din da ta gabata.
- Kasafin 2024: Gwamnan Gombe Ya gabatar da kasafin N207.8bn
- Jami’an DSS da masu gadi sun ba hamata iska a asibiti
Wani mazaunin yankin, Muhammad Yahaya, ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun isa unguwar ne a lokacin da mutane suka shiga masallaci domin yin sallar magariba.
Yahaya ya ce an yi awon gaba da mutum bakwai, sannan maharan sun harbi mutum daya da bindiga.
Lamarin na zuwa ne mako guda bayan da aka sace wani hakimin yankin, Chebawaza Sariki, amma daga baya aka sako shi a daren Asabar.
Haka kuma, kimanin wata guda, an sace mutum biyu a wasu yankuna biyu na Sherefe.
A baya-bayan nan hare-haren ’yan bindiga na ci gaba da kamari a wasu yankunan birnin tarayya, Abuja.