✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasafin 2024: Gwamnan Gombe Ya gabatar da kasafin N207.8bn

Shugaban majalisar, Abubakar Muhammad Luggerawo ya ba wa gwamnan tabbacin cewa za su duba Kasafin cikin a kan lokaci.

A ranar Linitin ne Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya mika wa majalisar dokokin jihar kasafin Naira biliyan 207.8 domin shekarar 2024.

Kasafin kudin ya kunshi Naira biliyan 87.25 na ayyukan yau da kullum, da kuma Naira biliyan 120.5 na manyan ayyuka.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce kasafin kudin wanda shi ne na farko a wa’adainsa na biyu ya kara da cewa manufarsa ita ce dorawa daga inda ya tsaya a wa’adin mulkinsa na farko.

Ya ce zuwa watan Satumba an aiwatar da kashi 57.4 cikin dari na kasafin 2023.

Gwamna Inuwa, ya hori Majalisa da ta duba kasafin da idon basira ta kuma yi dukkan abin da ya kamata da zai dace da bukatar al’umma.

Da yake jawabi, shugaban majalisar, Abubakar Muhammad Luggerawo ya ba wa gwamnan tabbacin cewa za su duba Kasafin cikin a kan lokaci.