✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsaftar Muhalli: An dawo da sharar karshen wata a Gombe

A ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Gombe take yi na tsabtace muhalli da kula da  lafiyar al'umma Gwamnan Jihar, Muhammad Inuwa Yahaya ya bada umurnin sake…

Gwamnatin Gombe ta dawo da sharar da ake yi a karshen kowanne wata da nufin tabbatar da tsaftar muhalli a fadin jihar.

Gwamnatin jihar ta ce manufar ta dawo da sharar a kowanne karshen wata ita ce tabbatar da kara kula da lafiyar al’umma da kuma tsaftar muhalli.

Kwamishinan Ruwa, Muhalli da Kula da Gandun Daji na jihar, Muhammad Sa’idu Fawu, ya bayyana cewa an ware duk ranar Asabar din ƙarshen wata a matsayin ranar shara a duk faɗin jihar, daga wannan wata na Afirilu.

Sanarwar ta ce za a dinga gudanar da sharar daga ƙarfe 8:00 zuwa 10:00 na safe, gami da taƙaita zirga-zirgar jama’a da ta ababen hawa.

Sannan ta umarci ɗaukacin jami’ai da ma’aikatun jihar da sauran jama’a su bi umarnin, tana mai cewa jami’an ma’aikatar da na Hukumar Kula da Tsaftar Muhalli (GOSEPA) za su sanya ido sosai don tabbatar da bin wannan umarni.