✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta sako wacce ta soki Gwamnatin Kaduna a Facebook

Aisha Galadima ta soki kalaman Gwamna Uba Sani na ƙarshe a kan El-Rufai ta shafinnta na Facebook

An sako Aisha Galadima, wacce take kare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da jami’an tsaron farin kaya (DSS) suka kama don yin bincike.

Aminiya ta ruwaito yadda aka damƙe ’yar Jam’iyyar APC  a Kaduna bisa wani rubutu da ta yi a Facebook kan Gwamna Uba Sani.

A cewar majiyoyi, Aisha Galadima ta soki kalaman Gwamna Uba Sani na ƙarshe a kan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.

Wata ƙwabciyarta ta ce, an kama ta ne a unguwar Tudun Wada a Kaduna a ranar Lahadi da yamma, kuma wata abokiyarta ta bayyana cewa wayar Aisha a kashe take bayan tsare ta da aka yi.

Sai dai babban sakataren yada labarai na gwamnan, Muhammad Lawal Shehu, ya ce ba shi da masaniyar kama ta.

“Ban san an kama wata mata da ta rubuta munanan kalamai a kan Gwamna ba. Amma kuna iya mika tambayoyinku ga hukumar DSS ba gwamnatin jihar Kaduna ba,” in ji shi.

Aminiya ta samu rahoton cewa, an sake ta ne bayan da ta kai kusan awa 24 a hannun hukuma.

Da aka tuntuɓi Aisha, ta tabbatar da sakin nata, inda ta ce jami’an hukumar sun tursasa tare dukan ta.

“Ina cikin dakina zan yi wanka sai suka shigo suka ja ni. Na ga motar su kirar Hilux hudu a wajen gidan. Suka tura ni ciki suka wuce,” in ji ta.

A cewarta, (DSS) sun zarge ta da yin wani rubutu a kan gwamnan a watan Fabrairu.