✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai

El-Rufai ya ce, yana da tabbacin ana cin zarafin abokin nasa ne saboda ya fice daga Jam’iyyar APC zuwa SDP.

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya fasa baragurbin ƙwai kan zargin sace Jafaru Sani, tsohon Kwamishina a gwamnatinsa.

El-Rufai, wanda ya mulki Jihar Kaduna daga 2015 zuwa 2023 kafin ya miƙa mulki ga Sanata Uba Sani, wanda shi ne ɗan takarar da ya fi so ya gaje shi, ya bayyana wannan batu ne a shafinsa na Facebook da aka tantance sahihancinsa a ranar Alhamis.

A cewarsa, an tsare tsohon Kwamishinan na shi ne a kurkuku ba bisa ƙa’ida ba.

El-Rufai ya ce, yana da tabbacin ana cin zarafin abokin nasa ne saboda ya fice daga Jam’iyyar APC zuwa SDP.

“An sace abokin aikinmu kuma tsohon kwamishina mai ƙwazo a zamanin mulkin El-Rufai, Malam Jafaru Sani, an sace shi ne a Kaduna da rana tsaka, yana ta hannun ‘yan fashin dajin Uba Sani da ke cewa su ’yan sanda ne!

“An tsare Jafaru a kurkuku ba tare da wata takardar sammaci daga ‘yan sanda ko ta tuhuma daga Ma’aikatar Shari’a ta Jiha ba.

“Bayan bincike, mun gano cewa ana zarginsa da safarar kuɗi. Amma ainihin laifin Jafaru shi ne ficewarsa daga APC zuwa SDP.

“Wannan salon zaluncin iri ɗaya ne da wanda aka taɓa yi wa wani abokinmu, Bashir Saidu, wanda aka sace a ranar 31 ga Disamba, 2024, aka tsare shi na tsawon kwanaki 50 kafin a bayar da belinsa!

“Rawar da wasu alƙalai ke takawa a shari’ar Kaduna abu ne mai matuƙar damuwa. Muna sa ido kuma muna jira domin babu wani yanayi da zai dawwama, kuma ranar hisabi za ta zo.”

Har yanzu gwamnatin Jihar Kaduna ba ta mayar da martani kan waɗannan zarge-zargen da El-Rufai ya yi ba.