✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutanen da ke hannu ana zargin mambobin ƙungiyar ta’adda ta Boko Haram ne da kuma na takwararta, ISWAP.

Jami’an Hukumar DSS sun cafke wasu mutum goma da ake zargi mambobin ƙungiyar Boko Haram ne a yankin Ilesa na Jihar Osun.

Malam Olawale Rasheed, mai magana da yawun gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Mallam Rasheed ya ce mutanen da ke hannu ana zargin mambobin ƙungiyar ta’adda ta Boko Haram ne da kuma na takwararta, ISWAP.

Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro tare da ba su goyon baya domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Osun.

Gwamna Adeleke ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su kasance masu sanya ido kan abin da ke faruwa a zamantakewarsu, tare da sanar da hukumomin tsaro da zarar sun ga wani abu da ba su gamsu da shi ba.

Gwamna Adeleke ya yaba wa ƙoƙarin jami’an tsaro kan yadda suka hanzarta ɗaukar mataki wajen kawar da barazanar ƴan ta’addan.