✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun halaka mayakan ISWAP da dama a Borno

Dakarun sojojin Najeriya sun dakile wani harin hadin gwiwa da 'yan ta'addar Boko Haram da ISWAP suka kai a yankin Marte da ke jihar Borno

Dakarun sojojin Najeriya sun dakile wani harin hadin gwiwa da ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP suka kai a yankin Marte da ke jihar Borno, inda suka kashe wasu da dama daga cikin maharan.

Majiyar leken asirin hedikwatar sojan Najeriya ta tabbatar  da cewa harin ya faru ne da misalin karfe 1:35 na wayewar safiyar talata 27 ga watan Mayu.

Majiyar ta ce wasu ’yan ta’adda da ba a tabbatar da adadin su ba sun kai hari a bataliya ta 50 da ke Marte.

Dakarun da ke samun goyon bayan wata tawaga ta runduna ta 24 da bataliya ta musamman ta 134, sun yi gaggawar fafatawa da ’yan ta’addan a wani kazamin fadan da aka kwafsa.

A cewar rahoton, dakarun rundunar sojojin saman Najeriya na Operation Hadin Kai, ta aiwatar da aikin leken asiri ta sama, da kuma dauki ba dadi, wanda ya taka rawar gani wajen fatattakar ’yan tada kayar bayan da suka tsere.

Majiyar ta ce sojojin sun yi nasarar dakile harin tare da dawo da cikakken iko a yankin, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin zakulo abubuwan da suka rage da kuma kwato makamai da kayan aikin da ’yan ta’addan ke amfani da su.

“Sojoji biyu sun rasa ransu a yayin wannan farmaki, sannan an samu wasu asarorin kayayyakin da suka hada da lalacewar wata babbar mota mai dauke da bindiga da kuma tayar wata motar sojoji,” in ji majiyar.

Harin na baya-bayan nan a Marte na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji ke dada kai hare-hare a yankin tafkin Chadi da arewacin Borno, inda kungiyoyin ISWAP da Boko Haram suka yi yunkurin sake kafa sansanoninsu.

A halin da ake ciki dai, ana ci gaba da sanya ido sosai kan harkokin tsaro a jihar Borno, inda ake ci gaba da gudanar da sintiri da tattara bayanan sirri da nufin hana kutse a nan gaba, in ji majiyar ta sojan Najeriya.