✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun tarwatsa matsugunin ’yan ta’adda da kashe wasu a Borno

Rundunar sojin sama ta gudanar da samamen ta ne a wani wuri da aka san shi da tudu mai tsauni, wanda ke kan iyakar Nijeriya…

Dakarun sojojin Nijeriya na rundunar sojojin sama tare da haɗin gwiwar Operation Haɗin Kai sun kai farmaki kan wasu muhimman wuraren da ’yan ta’adda suka mamaye a tsaunin Mandara da ke Jihar Borno.

An samu labarin cewa rundunar sojin sama ta gudanar da samamen ta ne a wani wuri da aka san shi da tudu mai tsauni, wanda ke kan iyakar Nijeriya da Kamaru, bayan samun bayanan sirri.

Daily Trust ta ruwaito cewa, samamen share fagen ya zo ne ƙasa da sa’o’i 24 da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya umurci sojoji da su kawar da duk maƙiya da ke barazana a ƙasar nan.

Kakakin rundunar sojin sama na Nijeriya, Ehimen Ejodame ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, aikin sa ido da binciken da sojojin ke yi ya ba da alamun cewa maharan na shirin kai hare-hare.

Air Commodore, Ejodame ya yi bayanin cewa matsugunin da suke amfani da shi mai amfani da lantarki da na’urar hasken rana da baƙaƙen tutoci, alama ce ta sake farfaɗowar maharan a wurin kafin a kai musu harin bam a tarwatsa su.

A cewarsa, manyan samamen, Wa Jahode da Loghpere, sun daɗe suna zama mafaka ga Ƙungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad (JAS), ɓangaren ’yan Boko Haram da ke da matsuninsu a can.

Ya ce, baya ga yadda aka tarwatsa matsunin ta sama da ya lalata kayan aikin ‘yan ta’addar, an kashe da dama daga cikinsu ciki har da kwamandojin su a harin.