Babban Mashawarcin Tsaro na Kasa, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa an kashe ’yan ta’adda sama da 13,000 a fadin Najeriya daga lokacin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hau mulki a watan Mayun 2023 zuwa yanzu.
Ribadu, yayin da yake jawabi a taron Koli na Jam’iyyar APC a zauren taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ya bayyana cewa duk da an samu ci-gaba mai sosai wajen magance matsalar rashin tsaro, yanayin sarƙaƙiyar tsaro ya sa a mafi yawan lokaci jama’a ba sa iya gane waɗannan nasarori nan take.
Ribadu ya bayyana cewa an kashe jimillar ’yan tada kayar baya da ’yan fashin daji 13,543, yayin ayyuka daban-daban da sojoji da sauran hukumomin tsaro suka gudanar a faɗin ƙasar.
Ya ƙara da cewa mayaƙan Boko Haram da ISWAP 124,408 sun miƙa wuya ga jami’an tsaro.
- Abin da muka sani kan labarin juyin mulki a Kwaddibuwa
- NAJERIYA A YAU: Dalilin ’Yan Adawa Na Ƙulla Ƙawance A Ƙarƙashin Inuwar ADC
“Tun da Tinubu ya hau mulki, lamarin ya canza, inda aka kashe shugabannin ’yan ta’adda da yawa. Sojojinmu sun kashe ’yan ta’adda 13,543,” in ji Ribadu.
Ya bayyana kalubalen tsaro da gwamnatin yanzu ta gada a matsayin “wanda ke barazana ga haɗin kai da zaman lafiya da mutuncin Najeriya. Akwai manyan hare-hare, manyan barna da kuma asarar rayuka masu yawa.”
Ribadu ya lissafa manyan barazanar da suka kasance a lokacin, ciki har da “Boko Haram, ISWAP, fashi da garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma, tayar da ƙayar baya a Kudu maso Gabas, Neja Delta da kuma rikicin makiyaya da manoma musamman a Arewa ta Tsakiya.”
Amma ya jaddada cewa duk da haka, an samu a fannin tsaro tun lokacin da gwamnatin yanzu ta hau mulki.