✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace fasinjoji 26 a hanyar Funtua-Gusau

Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji akalla 26 a wasu hare-hare guda biyu a kan hanyar Funtua zuwa Gusau.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji akalla 26 a wasu hare-hare guda biyu a kan hanyar Funtua zuwa Gusau.

’Yan bindigar sun sace fasinjoji 26 a kauyen Unguwar Boka da ke Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina.

Fasinjojin suna cikin motocin haya guda biyu ne — Hummer Haice da Sharon — sun nufi Gusau ne daga Funtua a lokacin da lamarin ya faru.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa hari na biyu ya faru ne a Gidan Kaji da ke kauyen Magazu, a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

A cewar majiyar, mazauna garin sun kasa tantance adadin fasinjojin da aka sace a Gidan Kaji amma an samu wata mota kirar Gulf Wagon a yashe a wurin, wanda hakan ya nuna cewa an yi garkuwa da dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin.

“Kwanaki uku da suka gabata ’yan bindiga sun kashe mutum daya suka sace wasu da dama a wurin.

“Mun lura sun mayar da wurin hanyaru kuma duk lokacin da za su wuce sai su yi awon gaba da masu wucewa,” in ji majiyar.

Gidan Kaji dai shi ne inda ’yan bindigar suka kashe wasu ’yan sanda da ke bakin aiki a wani shingen bincike a bara.