Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, ta lalata barasa da sauran muggan ƙwayoyi da ta ƙwace da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 60 a Ƙaramar Hukumar Funtua.
Kwamandan Hisbah na jihar, Dokta Aminu Usman ne, ya sanar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Katsina.
- Zan kori ’yan kasuwar da ke tsawwala farashin kayan abinci a masarautata — Ooni na Ife
- Gwamnatin Legas ta sake kulle Kasuwar Ilepo saboda ƙazanta
Ya ce sun ƙwace tare da lalata kwalayen giya 1,750 da jarkoki 33 na giya da aka sarrafa su a gida a Funtua.
Usman, ya bayyana cewa wannan aiki na daga cikin ayyukansu na inganta tarbiyy a jihar.
Ya jinjina wa ma’aikatan hukumar kan ƙoƙarinsu, inda kuma ya buƙace su da su ƙara azama wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Ya kuma roƙi shugabannin Addini a jihar da su tallafa wa hukumar, inda ya ce Hisbah ta kowa ce ba ta wani rukuni ba.
Usman, ya gode wa Gwamna Dikko Radda kan goyon bayan da yake bai wa hukumar.
Kazalika, ya buƙaci jama’a da su taimaka ta hanyar bayar da bayanai kan inda ake aikata ɗabi’u marasa kyau, sannan ya buƙaci iyaye, malamai, da shugabannin al’umma da su ƙara ƙaimi wajen koyar da matasa kyawawan halaye.