✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta nemi NLC ta janye zanga-zangarta kan tsadar rayuwa

Hukumar tsaro ta DSS ta bukaci kungiyoyin kwadago su janye zanga-zangar da suka shirya kan tsadar rayuwar da ke addabar ’yan Najeriya

Hukumar tsaro ta DSS ta bukaci kungiyoyin kwadago su janye zanga-zangar da suka shirya gunadarwa fadin Najeriya kan tsadar rayuwar da ke addabar yan Najeriya.

Hukumar ta DSS ta ce duk da cewa kungiyar na da hakkin gudanar da zanga-zangar a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu, amma rokon nata na neman zaman lafiya ne a fadin kasar da kuma kauce wa tada zaune tsaye.

Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya bukaci shugabannin kungiyoyin kwadagon da su tattauna da jami’an gwamnati.

Bayan taronta na majalisar zartarwar kungiyar kwadagon ta kasa a Abuja ranar Juma’a  ne suka sanar cewa za su gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu a fadin kasar saboda gwamnati ta saba yarjejeniyoyin da suka cimma a watan Oktoban 2023.

Sai dai Afunanya ya bayyana cewa zanga-zangar za ta kara tayar da hankali a kasar, yana mai cewa, a iya sanin hukumar DSS, gwamnati a dukkan matakai na kokarin ganin an daidaita yanayin tattalin arzikin, don haka ya kamata a yi la’akari da hakan.

Ya kuma yi zargin cewa wasu marasa kishi na shirin amfani da zanga-zangar wajen haifar da rikici a kasar don haka na jaddada bukatar sake yin tunani domin guje wa abin da zai kawo barazana ga zaman lafiya tare da mummunan sakamako.

“Hakazalika, ana roƙon iyaye da masu kula da su da su yi amfani da su ja hankakalin ya’yansu su guji munanan ayyukan da za su iya kawo cikas ga zaman lafiya.