An gano gawarwakin wasu mutum takwas da ake zargin ‘yan bindiga ne bayan da sojoji suka kai samame wasu dazuka a ƙauyen Kurutu da ke kusa da Azzara a ƙaramar hukumar Kachia a Jihar Kaduna.
Aminiya ta ruwaito cewar sojoji sun kai hari sansanin ‘yan bindiga biyu da ke kewayen Kurutu da Hayin-Dam, waɗanda ke kan iyaka da Kagarko da Kachia a ranar Juma’ar da ta gabata.
- DAGA LARABA: Dabarun Kauce Wa Dagulewar Lissafi Sakamakon Ruwan Sama
- Zanga-zanga: Majalisar Koli Ta Shari’ar Musulunci Ta Gargadi Matasa
Rahotanni sun bayyana yadda ‘yan bindiga da dama suka tsere da raunuka bayan yin arangama da dakarun sojoji.
Wani ɗan banga daga ƙauyen Kurutu, wanda aka bayyana sunansa da Abdullahi, ya ce wasu manoman yankin sun gano gawar mutum takwas a ranar Litinin a kusa da Hayin-dam.
Ya ce da samun bayanin, wasu ’yan banga daga Kurutu da Hayin -dam, suka isa dazukan don ganin gawarwakin.
Ya ce, “A ranar Litinin, da misalin ƙarfe 11 na safe, wasu manoma da suka je gona, sun ga wasu gawarwaki da raunin harsasai kuma ana kyautata zaton maharan da sojoji suka kai wa samame ne a Kurutu da Hayin-dam a ranar Juma’a.”
Wani shugaban yankin, ya tabbatar da gano gawarwakin, ta wayar tarho a ranar Talata.
Ya ce, “Wasu manoman da suka je gona sun dawo gida da labarin cewar sun ga gawarwaki da harsasai a dajin, na kuma sanar da wasu ’yan banga. Sun je sun yi min bidiyo domin ganin gawarwakin.”
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, har yanzu bai ce uffan ba game da lamarin ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.