Dakarun sojin Najeriya da ‘yan banga sun ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su a sansanin ‘yan Boko Haram da ke garin Kanama a karamar hukumar Damboa da kuma garuruwa Imimi da Bulabulin a karamar hukumar Konduga a jihar Borno.
Wasu majiyoyin leken asiri sun shaidawa Zagazola Makama cewa an gudanar da wannan samame ne a ranar 18 ga watan Yulin 2024 bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ta’addan a yankin baki daya.
Majiyar ta ce, sojojin sun gano wani katafaren sansanin Boko Haram a Imimi Bulabulin, inda suka yi galaba a kan ’yan ta’addan, suka kashe daya daga cikinsu yayin da wasu suka tsere.
Sojojin sun kuma lalata wasu sansanoni, suka kwato wasu kekuna 11, da akwatunan harsasan AK 47 guda 2, da sauransu.
Sun kuma ci karo da wasu mutane bakwai da aka garkame su a cikin sarka a wani sansanin a kauyen Kanama.
Wadanda aka ceto, dukkansu Fulani makiyaya ne da suka yi ikirarin cewa an yi musu fashi da garkuwa da su a lokuta da wurare daban-daban.