✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta kwace N1.5bn daga tsohon shugaban NIRSAL

Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin kwace Naira biliyan 1.58 daga tsohon Manajan Darakta na Hukumar NIRSAL, Aliyu Abatti Abdulhameed.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin wucin gadi na kwace Naira biliyan 1.58 da ake alakantawa da tsohon Manajan Darakta na Hukumar ba da Rancen Noma (NIRSAL), Aliyu Abatti Abdulhameed.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya umarci Hukumar EFCC wadda ke karar tsohon shugaban na NIRSAL ta da wallafa umarnin a jarida, domin jin ko akwai wani mai hujjar da za ta hana kotun ba da umarnin dindindin na kwace kudaden, cikin kwanaki 14.

Alkalin ya ba da umarnin nen bayan EFCC ta gurfanar da Abdulhameed da Dokta Steve Olusegun Ogidan da mukarrabansu kan haramtattun kudaden da hukumar ta kwato daga hannunsu.

A ranar 5 ga Fabrairu, 2024 kotun  ta ba da umarnin wanda wakilinmu ya samu gani a ranar Talata.

Lauyan EFCC, GI Ndhe Esq, wanda ya gabatar da bukatar, ya ce kotun ta bayar da umarnin damka wa gwamnatin tarayyar kudi Naira biliyan 1,582 da aka samu wadanda ake zargi sun same su ne ta  haramtacciyar hanya.

A karshe alkalin ya dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 20 ga watan Maris.