’Yan bindiga sun sace wasu dalibai mata a dakunan kwanansu a Jami’ar Tarayya ta Dutisnma da ke Jihar Katsina.
Aminiya ta gano cewa da sanyin safiyar Laraba ne ’yan bindiga suka kutsa dakunan kwanan daliban da ke kusa da Kasuwar Labara suka yi awon gaba da daliban.
- DAGA LARABA: Me Ya Sa Waɗanda Suka Kammala Jami’a Ke Komawa Sana’ar Girke-Girke?
- A gaggauta kuɓutar da sauran ɗaliban jami’ar da aka sace a Gusau — Tinubu
Jami’in Hulda da Jama’a na jami’ar, Habibu Umar Aminu, ya shaida wa wakilinmu cewa da misalin karfe 2 na dare ne aka yi garkuwa da daliban kuma ana kokarin ganin sun kubutar da su.
Kimanin mako biyu ke nan da wasu ’yan bindiga a Jihar Zamfara sau suka sace dalibai mata na Jami’ar Tarayya ta Gusau, kuma har yanzu da sauran daliban a hannunsu.
Wani dalibin jami’ar FUDMA ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa “dalibai biyar din da aka yi garkuwa da su sun fito ne daga jihohin Kano da Nasarawa kuma biyu daga cikinsu ’yan ajin karshe ne.”
Kawo yanzu dai ba a ji daga maharan ba, amma daliban jami’ar ta FUDMA sun shaida wa wakilinmu cewa tun bayan harin da aka sace dalibai a Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS) a Jihar hukumar gudanarwar FUDMA ta bukaci dalibai da su daina fita bayan karfe 10 na dare.
Kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, ASP Sadiq Aliyu Abubakar, ya ce an rundunar ta cafke wani wanda ake zargi da yi wa ’yan bindigar leken asiri da suka yi amfani da su wajen sace daliban.
Jami’in wanda ya tabbatar cewa ana kokarin ceto daliban ya kar da cewa wasu mutane da ake zargi da hannu a lamarin suna hannun rundunar.