Wasu ’yan bindiga a ranar Litinin sun yi kwanton bauna sannan suka kashe ’yan sanda hudu a kusa da wani shingen bincike da ke hanyar Gusau zuwa Bungudu a Jihar Zamfara.
’Yan sandan da aka kashe dai suna aiki ne a ofishin ’yan sanda na Karamar Hukumar Bungudu, kuma sun kafa shingen ne a wajen da aka yi musu kwanton baunar.
- Majalisar Dokokin Bauchi za ta fara amfani da Hausa a yayin zamanta
- Cutar Diphtheria ta kashe yara 30 a Yobe
Bugu da kari, ’yan bindigar sun kuma kai hari kauyen Tagero, inda suka sace shanu da dama.
A ’yan kwanakin nan dai, ’yan bindiga sun matsa da kai hare da kuma satar mutane a Jihar.
Maharan sun kuma sace manoma da yawa da ke aiki a gonakinsu tun bayan faduwar saminar bana.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da kai harin ga Aminiya, inda ya ce yanzu haka ma an tsaurara matakan tsaro a yankin.