✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya taƙaita ayarin motoci 3 ga Ministoci

Matakin da ya ce wani ɓangare ne na ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na rage kashe kuɗaɗen gudanar da mulki.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taƙaitawa Ministoci da Shugabannin Hukumomin Gwamnatin Tarayya, ayarin motocinsu kar su wuce motoci uku.

Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis ya ce, “Ba za a ba su ƙarin motoci don zirga-zirga ba.”

Matakin da ya ce wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin tarayya na rage kashe kuɗaɗen gudanar da mulki duba da irin abubuwan da ke faruwa.

A watan Janairu, Tinubu ya ba da umarnin cewa, yin hakan zai rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa, ya kamata a rage yawan masu tafiya zuwa ƙasashen waje daga 50 zuwa 20; da 25 don balaguron cikin gida.

Hakazalika ya rage tawagar mataimakin shugaban ƙasar zuwa jami’ai biyar a tafiye-tafiyen ƙasashen waje da jami’ai 15 na tafiye-tafiyen cikin gida.

A cikin umarnin da ya bayar a yau, Shugaba Tinubu ya kuma umarci dukkan ministocin da shugabannin hukumomin gwamnati da su sanya jami’an tsaro aƙalla biyar su kasance tare da su.

“Tawagar jami’an tsaron za ta ƙunshi ‘yan sanda huɗu da jami’in tsaron farin kaya na DSS guda ɗaya. Ba za a ba da ƙarin jami’an tsaro ba,” kamar yadda ya ba da umarnin.