✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɓarayin “One chance” sun kashe matashiya a Abuja

Sun kashe matashiyar bayan karɓar sama da Naira miliyan ɗaya a hannun uban gidanta.

Wata matashiya mai shekara 28 mai suna Na’ima Suleiman, ta gamu da ajalinta a hannun ɓarayin “One Chance” bayan ta shiga motarsu a babbar hanyar Kubwa da ke Abuja.

Mahaifin marigayiyar, Alhaji Suleiman Abdullahi, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin.

“Shugabansu na wajen aiki ne ya ɗauko ta da wasu sauran abokan aikinta ya ajiye su a mahaɗar Banex da ke Abuja da misalin ƙarfe 6 na yamma, bayan sun tashi daga aiki.

“A can ne kowanensu zai shiga motar da za ta kai shi gida.”

Ya ƙara da cewa, “Shugaban nasu ne ya zo nan gida ya faɗa min cewa bai wuce minti 10 da ajiye su ba sai ya ga kiranta.

“Bayan ya ɗaga wayar sai ta faɗa masa cewa a halin yanzu tana hannun masu garkuwa da mutane. Nan take ya ce mata ta ba su wayar ya yi magana da su,” in ji shi.

Har wa yau, ya yi ƙarin haske cewa, “Bayan ya yi magana da su sai suka faɗa masa ba za su sake ta ba har sai an biya su miliyan ɗaya.

“Ya amince zai ba su kuɗin amma ka da su yi mata komai. Take kuma suka tura masa lambar asusunta, ya tura musu kuɗin.”

Mahaifin matashiyar ya bayyana cewa bayan sun karɓi kuɗin sai suka kashe ta suka jefar da gawarta a kan gadar sama ta unguwar Minister’s Hill.

Daga bisani ’yan sanda, suka tsinci gawarta da daddare suka kai ta Babban Asibitin Abuja, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta.

Mahaifin, ya bayyana wa Aminiya cewa kawo yanzu babu wanda aka kama kan lamarin amma ’yan sanda suna gudanar da bincike.

Marigayiyar ta yi digiri a Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa, kuma ta kusa kammala karatun digiri na biyu.

Kafin rasuwar matashiyar, ta kasance ma’aikaciya a kamfanin Half Dollar da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.