✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dokokin Bauchi za ta fara amfani da Hausa a yayin zamanta

Za a rika amfani da Hausa a matsayin harshe na biyu

Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta amince ta fara amfani da Hausa a matsayin harshe na biyu da za ta rika amfani da shi a yayin zamanta.

Kakakin Majalisar, Abubakar Y. Suleiman, ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar na ranar Talata.

Hakan dai ya biyo bayan kudurin da dan majalisa mai wakiltar mazabar Shira, Auwal Hassan ya gabatar da bukatar amfani da harshen, kari a kan Hausa.

A cewar dan majalisar, duk da cewa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba da uamrnin yin amfani da Turancin Ingilishi yayin ayyukan majalisar, amma sadara ta uku ta doka ta 8 ta amince za a iya amfani da wani harshen daga cikin wadanda ake amfani da su a Jihar, idan ’yan majalisar sun amince.

Ya ce kasancewar Hausa harshen da aka fi amfani da shi a Jihar, inda kusan kaso 90 na mutanen jihar ke amfani da shi.

Da yake goyon bayan kudurin, dan majalisa mai wakiltar mazabar Bogoro, Musa Wakili Nakwada, ya yaba wa Auwal saboda gabatar da kudurin, inda ya ce hatta majalisar da ta gabata ita ma ta yi smfsni da Hausar.

Bayan Kakakin majalisar ya gabatar da kudurin ne sai ’yan majalisar suka amince da shi da murya daya.